in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'ivoire za ta karbi bakuncin wasannin kungiyar ECOWAS karo na uku
2013-06-20 13:56:06 cri

Yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a ranar Laraba a birnin Abidjan tsakanin kwamitin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS da gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ta shafi batun shirya wasannin kungiyar ECOWAS na karo na uku a kasar Cote d'Ivoire da ake tsai da yi a shekarar 2014. Ministan kula da dunkulewar Afrika na kasar Cote d'Ivoire, Ally Coulibaly da shugaban tawagar kungiyar ECOWAS, Desire Kadre Ouedraogo, suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya a madadin gwamnatin kasar Cote d'Ivoire da kuma kungiyar ta shiyyar yammacin Afrika.

Wasannin kungiyar ECOWAS na shekarar 2014 za su kasancewa bisa wasannin shida da suka hada da wasannin guje-guje, kakowa, wasannin kwallon hannu da na kwallon raga, wasan dambe da kuma kwallon kwando.

Wasannin motsa jiki sun kasance wata babbar hanya da ta hada kan al'ummomin kasashen Afrika, in ji mista Ouedraogo dake fatan ganin dukkan kasashe goma sha biyar na wannan kungiya za su amsa kiran wadannan wasanni da za'a shirya a kasar Cote d'Ivoire.

Wasannin kungiyar ECOWAS karo na biyu sun gudana a birnin Accra na kasar Ghana daga ranakun 16 zuwa 22 ga watan Yunin shekarar 2012 tare da samun halartar kasashe goma sha daya da suka fafata cikin wasannin biyar, kana wasannin karon farko sun gudana a cikin watan Satumban shekarar 2010 a birnin Abuja na Najeriya tare da halartar kasashe goma wadanda suka fatata cikin wasanni hudu.

Wasannin kungiyar ECOWAS na bisa tsarin hangen kungiyar ECOWAS a shekarar 2020 wato sauya manufar ECOWAS ta kasashe zuwa ECOWAS ta al'ummomi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China