Hukumar yaki da bazuwar kananan makamai a kasar Kwadibwa (COMNAT-ALPC), ta bayyana ranar Laraba cewar, an tura jami'an cibiyar sa ido kan alamun barkewar rikici, (OVA) a fadin kasar baki daya.
A cikin watan Disambar bara, hukumar ta kafa wannan cibiyar dauke da manufar cimma shirye-shiryenta.
A cikin wata sanarwa, hukumar COMNAT-ALPC ta bayyana cewa, bayan da aka kammala gwajin wannan shiri, ana kokarin fadada aikin zuwa al'umomi da garuruwa guda 107.
An yi wa jami'an horaswa kan yadda za su taro bayanai, su rubuta, su kuma tsara su ta wani fasali, da kuma aikawa da bayanin domin a samu tabbatar da bayani ko kuma yanayi da aka samu barkewar rikici.
Mataimakin babban sakataren hukumar Anzian Kouadja ya ce, za'a shirya wasu tarukan samar da horo, a cikin watanni uku masu zuwa, domin cibiyar ta samu isa fadin kasar baki daya, ta kuma taimakawa gwamnati a kan yaki da safara da kuma bazuwar kananan makamai ba bisa ka'ida ba, a kasar baki daya. (Lami)