Wata majiya a hukumance a kasar Cote d'Ivoire ta bayyana a ranar Laraba yayin bikin ranar yaki da ci ga gumin yara na duniya cewa, sama da yara 46,000 masu a kalla shekaru 14 ne ke ayyuka a cikin gida a kasar Cote d'Ivoire.
Ministan kwadago da harkokin jin dadin jama'a na kasar Moussa Dosso ya bayyana cewa, ana shirin bullo da wata dokar da za ta karfafa yaki da ci da gumin yara.
Dosso ya ce, kamata ya yi hukumomi su kara daukar matakai don tabbatar da cewa, an kawar da ta'addar ya zuwa shekara ta 2016.
A cewar ministan, gwamnati za ta gudanar da kamfel din ilimantar da jama'a tare da kafa kwamitin da zai sa ido kan irin ci gaban da aka samu game da yaki da wannan mummunar al'ada.
Jami'in ya ce, wajibi ne gwamnati ta tabbatar da cewa, yaran da ke kasar su ci gajiyar ilimi lafiya da kuma jin dadin rayuwarsu. (Ibrahim)