Jam'iyyar al'ummar kasar Cote d'Ivoire (FPI) ta tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo ta gyayyaci gwamnatin kasar Cote d'Ivoire da ta kafa wani yanayi mai kyau cikin gaggawa domin fara tattaunawa bayan da ta samu takardar gayyata daga hannun faraministan kasar na fara yin shawarwarin kai tsaye tsakanin gwamnati da babbar jam'iyyar adawa, ta yadda za'a samar da yanayin siyasa mai kyau bayan rikicin zabe na shekarar 2010-2011.
Jam'iyyar FPI na fatan ganin gwamnati ta kafa ba tare da bata lokaci ba bisa kuma nauyin dake bisa wuyanta wani yanayin da ya dace da zai iyar kawar da sabane-sabanen dake hana ruwa guda wajen tabbatar da zaman lafiya da demokaradiya, in ji sanarwar wannan jam'iyya.
A cewar FPI, rashin jituwar da ake samu, na da nasaba da yanayin fargaba na sace-sacen mutane, tsare mutane gidajen yari da farautar magoya bayan 'yan adawa a ko da yaushe, da rashin adalci ta fuskar shari'a daga wajen masu mulki tare kuma da hana kafofin gwamnati yin aikinsu yadda ya kamata. (Maman Ada)