Kakakin gwamnatin kasar Cote d'Ivoire Bruno Kone ya ba da sanarwa a ranar Talata a birnin Abidjan cewa, gwamnatin kasar da 'yan adawa na kasar na shirin koma wa teburin shawarwari ba da jimawa ba. Mista Kone dake hira tare da manema labarai ya bayyana cewa, hukumomin kasar a shirye suke domin fara tattaunawa tun daga bakin ranar Litinin 24 ga watan Yuni.
'Ba'a yanke shawarwarin ba. Muna rike da tuntubar juna tare da jam'iyyun adawa da kungiyoyin adawa.' in ji mista Kone, tare da jaddada cewa, wannan muhimmiyar haduwar da za'a sanya ta bisa tushen imani da bude kofar jituwa. (Maman Ada)