A jiya Alhamis 4 ga wata, aka rantsar da babban alkalin kasar Masar Adli Mansour a matsayin sabon shugaban kasar na rikon kwarya bayan hambarar da shugaba Mohammed Morsi daga karagar mulki.
A safiyan wannan rana, Adli Mansour ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban babbar kotun tsarin mulki. Yana mai bayanin a cikin jawabin fara aikinsa cewa, shawarar rantsar da shi a matsayin shugaban rikon kwarya ya fito ne daga wadanda ke da ikon yin hakan kadai wato al'ummar kasar Masar.
Zanga-zanga ta gama gari da jama'a suka yi a kasar baki daya domin nuna kiyayyarsu ga mulkin jam'iyyar 'yan uwa musulmi wato 'Muslim Brotherhood' tun ranar lahadi 30 ga watan Yuni zuwa ranar Laraba 3 ga watan Yuli ta sanya sojoji hambarar da Mohammed Morsi tare da nada Adli Mansour ya jagoranci kasar na wani dan lokaci.
Sojojin kasar sun kuma shimfida wani tsari na mika mulki hannun farar hula wanda a ciki, za'a kafa wata gwamnatin hadaka da za ta fadada ikonsa, sun kuma dakatar da kundin tsarin mulkin kasar na yanzu tare da kafa wani kwamiti da zai duba bukatun jama'a wajen yin kwaskwarima ga sabon kundin tsarin mulki. (Fatimah)