in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Snowden ya amincewa samun mafaka a Venezuela, in ji 'dan majalisar Rasha
2013-07-10 10:38:39 cri

Ma'aikacin liken asirin kasar Amurka Edward Snowden ya amince ya karbi mafakar siyasa daga kasar Venezuela, in ji wani babban 'dan majalisar kasar Rasha, ranar Talatar nan.

A shafinsa na internet na Twitter, shugaban kwamitin harkokin kasa da kasa a karamar majalisar dokokin kasar Rasha Alexei Pushkov ya bayyana cewa, kamar yadda suka sa ran gani, Snowden ya amince da dama da shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro ya ba shi ta samun mafakar siyasa.

Ya kara da cewa, Snowden na mai ganin wannan tayi ya dace.

To amma kuma daga baya an cire wannan bayani daga shafin internet din, kana Pushkov ya bayyana a wani sabon sako da ya sanya a shafin nasa cewar, ya samu labarin amincewa da Snowden ya yi ne daga labaru da tashar talbijin ta channel Vesti 24 ta kasar Rasha ta bayar.

A karshen makon da ya gabata, kasashen Venezuela, Nicaragua da Bolivia duka sun baiwa Snowden damar samun mafakar siyasa.

A kuma ranar Litinin, shugaban kasar Venezuela, Maduro ya ce, kasarsa ta samu wasikar neman samun mafakar siyasa daga Snowden, don haka za su tsai da kuduri kan cewar, idan ya taso a jirgin sama, ko zai sauka ne cikin kasar. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China