A ranar 5 ga wata, shugaban kasar ta Venezuela Nicolas Maduro ya sanar da bai wa Edward Snowden mafakar jin kai a hukumance. Ya yi wannan furuci ne a bikin tunawa da zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar a wannan rana. Ya kara da cewa, Edward Snowden ya fallasa shirin gwamnatin Amurka na satar jin bayanai da sadarwar intanet na jama'ar kasa da kasa, don haka bai keta dokoki ba.
Ban da wannan kuma, shugaba Maduro ya jaddada cewa, wasu kasashen da ke yankin Latin Amurka sun nuna masa cewa, za su kasance a bangaren Venezuela kan batun Edward Snowden. A wannan rana kuma, shugaba Daniel Ortega Rosales na kasar Nicaragua ya ce, kasarsa ita ma tana son bai wa Edward Snowden mafakar siyasa. (Tasallah)