in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abokan hamayyar Mugabe sun yi watsi da wa'adi kan lokacin zaben Zimbabwe
2013-06-06 10:06:24 cri

A ranar Laraba, manyan jam'iyyun siyasa biyar na kasar Zimbabwe, wadanda ba su cikin jam'iyyar Zanu-PF ta shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, sun shiga kiran yin watsi da wa'adin lokacin gudanar da zabe da kotun dokokin kasar ta bayar a makon da ya wuce.

Jam'iyyun sun ce, ranar 31 ga watan Yuli, ba lokaci ne mai yiwuwa ba, kuma wajibi a fara aiki da sauye-sauye da aka bullo da su kafin lokacin zaben domin a tabbatar da zabe cikin adalci kuma na bai daya, wanda ya hado zaben shugaban kasa, na 'yan majalisa da kuma na yankuna.

Zaben zai kawo karshen gwamnatin gamayya ta tsawon shekaru hudu, wacce ta gagara samun daidaito. Shugaba Mugabe mai shekaru 89 kuma shugaba mafi tsufa a Afirka zai sake tsayawa takara. Babban abokin hamayyarsa kuma fraministan kasar Morgan Tsvangirai, 'dan shekaru 61, shi ne mai jagorantar babbar jam'iyyar adawa ta 'Movement for Democratic Change' (MDC).

Sauran kananan jam'iyyun kamar ZAPU, MKD da Zanu-Ndonga sun bayyana cewa, sun amince da ra'ayin jam'iyyar MDC cewa, kara da mutum daya ya shigar kotu ne sanadin yanke ranar zaben wanda kuma ake ganin ya take 'yancin miliyoyin 'yan kasar Zimbabwe a fuskar shiga zabe ba tare da magudi ba.

Bangarorin sun amince za su gabatar da korafinsu yayin wata ganawa ta musamman ta kungiyar bunkasa al'ummar kudancin Afirka ranar 9 ga watan Yuni wanda kuma zai mai da hankali kan zaben na kasar Zimbabwe. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China