in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Zimbabwe ya yi barazanar kauracewa zabe
2013-06-13 09:47:14 cri

A ranar Laraba, firaministan kasar Zimbabwe Morgan Tsvangirai ya yi barazanar kauracewa babban zabe na kasar wanda za'a yi ran 31 ga watan Yuli, muddin ba'a aiwatar da sauye-sauye a kafofin watsa labarai da na tsaro a kasar ba.

Har yanzu, shugaba Robert Mugabe wanda yake gwamnatin hada kai da tsohon abokin hamayyarsa Tsvangirai, bai bayyana ranar da za'a gabatar da zaben shugaban kasa, da 'yan majalisa da kananan hukumomi ba. To amma dai babbar kotun kasar ta yanke hukunci cewa, ba za'a yi zabe ba bayan 31 ga watan Yulin shekarar 2013.

Jam'iyyar Mr. Tsvangirai ta jadadda cewa, tana yiwuwa a samu rashin adalci a zaben saboda kafofin watsa labaran kasar da rundunonin tsaro duka suna goyon bayan shugaba Mugabe ne.

Tsvangirai ya bayyana wa shuwagabannin kungiyoyi yayin wata ganawa a birnin Harare cewa, shugaban ba zai bayyana ranar zaben ba, ba tare da tuntubarsa ba domin dukkansu kusoshi ne a gwamnatin. Firaministan ya kuma kara da cewa, zai shawarci shugaban kasar da ya daga zaben duk da hukunci da kotu ta yanke.

A halin da ake ciki kuma kungiyar bunkasa kudancin Afirka (SADC) ta sanar da cewa, za ta yi taro na musamman a karshen wannan mako a Maputo, babban birnin kasar Mozambique don tattaunawa kan batun shirye-shiryen kasar Zimbabwe dangane da zabe. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China