in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben Zimbabwe ta ce, ta shirya gudanar da babban zabe
2013-06-05 10:41:27 cri

Hukumar zaben kasar Zimbabwe a jiya Talata 4 ga wata ta sanar da cewa, ta kammala shirinta na gudanar da babban zabe a ranar 31 ga watan Yuli idan har shugaban kasar Robert Mugabe ya ba da umurnin haka.

Sai dai kuma hukumar ta fitar da tsarin da za'a bi wajen yin zaben wanda shi ne yake da wuyar cimmawa kafin 31 ga watan na Yulin kamar yadda kundin dokar kasar ya tanadar a makon da ya gabata.

A kalla ya kamata a samu kwanaki 14 tsakanin sanar da ranar zaben da kuma zaman nada kotun da za ta duba hakan, sannan kuma kwanaki 30 ake bukata tsakanin tsai da ranar da kotun ta yi da takamammen ranar zaben.

Kundin dokar kasar ta tanadi kwanaki 30 na aiki tukuru domin daukan sunayen wadanda suka cancanci kada kuri'a wanda a da aka tsara fara shi a Litinin din makon nan, amma yanzu an matsar da shi zuwa gaba.

Shugabar hukumar zaben mai zaman kansa na kasar Madam Rita Makarau ta ce, tantance masu kada kuri'a za'a kammala shi kwanaki biyu kamin zaman kotun tantancewar.

Masu adawa da shugaba Mugabe, wato firaministan kasar Morgan Tsvangirai da ministan masana'antu da kasuwanci Welshman Ncube sun ki amincewa da ranar 31 ga watan Yuli a matsayin ranar zabe, suna masu cewa, lokacin ya yi kadan da za'a yi duk gyaran da ake bukata da za'a tabbatar da kada kuri'ar cikin adalci da gaskiya.

Shi shugaba Mugabe ya ce, zai bi hukuncin da shari'a ta yanke a kan batun. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China