in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Zimbabwe zai kalubalanci shugaba Mugabe game da tsai da ranar zabe
2013-06-13 20:37:56 cri
Firaministan Zimbabwe Morgan Tsvangirai a yau Alhamis 13 ga wata ya ce, zai kalubalanci abokin hamayyarsa a tsawon lokaci shugaba Robert Mugabe a babban kotun kula da tsarin mulki a kan tsai da ranar zabe da ya yi na ran 31 ga watan Yulin bana.

Tsvangirai ya bayyana a wani taron manema labarai cewar, Mugabe ya aiko mashi a rubuce a farkon wannan rana cewar, ya tsayar da ranar 31 ga watan Yuli a matsayin ranar zabe, inda Tsvangirai ya ce, ba zai amince da wannan rana ba, yana mai nuna shakkunsa game da lokacin.

Tsvangirai dai a wani bangaren yana son a kara lokaci a kuma yi wassu sauye-sauye kafin gudanar da wannan zabe, a kalla nan da watan Augusta na bana.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China