Yan adawar Syria sun bayyana a ranar Lahadi cewa, sun amince bisa manufa su halarci tattaunawar zaman lafiyar da za a yi a birnin Geveva.
Babban jami'in kungiyar galibinsu mazauna ketare(SNC) Louay Safi ya shaidawa manema labarai a Istanbul na kasar Turkiya cewa, shugaba Bashar al-Assad ba zai kasance a cikin maganar makomar Syria ba.
Ya kuma ce, suna maraba da shirin kasa da kasa na samar da zaman lafiya a kasar, kuma duk wani kokari na samun nasarar shirin wajibi ne ba za a sanya shugaba mai ci a ciki ba.
Tun a ranar Alhamis ne babbar kungiyar adawa ta Syria, ta gudanar da tattaunawa a Istanbul don bayyana matsayinta game da taron wanzar da zaman lafiya karo na biyu game da Syria da za a yi a Geneva
Bugu da kari, yayin taron na Istanbul, ana sa ran kungiyar ta SNC ta zabi sabon shugabanta wanda zai maye gurbin Moaz al-Khatib wanda ya sauka daga mukaminsa a watan Fabrairu. (Ibrahim)