Alh. Shettima ya ce, a lokacin da ziyara a nan kasar Sin, ya ce, aikin gona na zamani na kasar Sin ya burge shi sosai, kuma a ganinsa, dalilin da ya sa aikin gona na Sin ya cimma nasara shi ne sabo da injunan zamani da irin hatsi mai kyau, da kuma takin zamani mai inganci da kasar Sin take da shi. A cikin shekaru goma-gomai, Sin ta warware matsalar samar da abinci ga al'ummar kasar da yawansu ya kai biliyan 1 da wani abu, kana ta kawar da talauci da yunwa da aka yi fama da su, sabo da haka, jihar Borno tana fatan koyon fasahohi daga kasar Sin, don ci gaba da inganta hadin gwiwa wajen aikin gona da kasar Sin, ta haka, za a iya warware matsalar noman rani da ke ci wa jihar tuwo da kwarya.
Ban da wannan kuma, Gwamnan ya bayyana cewa, yana fatan inganta hadin gwiwa da kamfanonin samar da na'urori masu amfani da hasken rana don samar da wutan lantarki na kasar Sin, don samun damar warware matsalar wuta a kuma raya aikin gona na zamani a jihar.(Bako)