Yayin da daya daga cikin 'yan wasan kasar Nijeriya Abubakar Usman ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, duk da cewa, a zangon Lanzhou, kungiyar wasan kwallon kwando ta Nijeriya ta lashe kungiyar ta Sin, amma ya ce, irin sakamakon gasar ba ya da muhimmanci sosai, abin da ya fi muhimmanci shi ne, a yi amfani da gasar don kara dankon zumunci da ke tsakanin kasashen Nijeriya da Sin, da kara kwarewar wajen wasanni.
Ban da wannan kuma, Abubakar ya jinjinawa kokarin da kasar Sin ta yi wajen karbar bakunci gasar. Ya ce, zangon Lanzhou da na Guangzhou, masu shirya gasar sun yi aiki ainun, abun da ya sa 'yan wasan jin dadin zama tamkar a gida. Ya kuma nuna godiya ga masu shirya gasar, yana fatan tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da habaka, kuma zaman rayuwar jama'a zai kara samun kyautatuwa.(Bako)