Dangane da sanarwar da tsohon firaministan kasar Pakistan, Nawaz Sharif ya bayar kan cewa, Jam'iyyar Pakistan Muslim League dake karkashin jagorancinsa ta samu rinjaye a zaben majalisar dokokin kasar, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hong Lei, ya bayyana a Litinin 13 ga wata, a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin tana farin ciki ganin cewa an gudanar da babban zabe yadda ya kamata a kasar Pakistan, kuma sakamakon farko ya sheda cewa, jam'iyyar PML da shi Sharif ke jagoranta tana kan gaba.
A don haka Kasar Sin tana nuna matukar farin cikinta kan wannan sakamako ga kasar Pakistan. A matsayin abokiyar Pakistan, a ko da yaushe, kasar Sin za ta tsaya kan tallafawa kasar Pakistan kan kokarinta na tabbatar da kwanciyar hankali da samun ci gaba.(Bello Wang)