in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mandela na cikin mawuyacin hali
2013-06-24 10:11:36 cri

Fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta fada a ranar Lahadi cewa, tsohon shugaban kasar mai shekaru 94 Nelson Mandela, yana cikin mawuyacin hali.

Kakakin shugaba Jacob Zuma na kasar Afirka ta Kudu, Mac Maharaj ya ce, shugaba Zuba ya ziyarci Mandela a asibitin Pretoria a ranar Lahadi kuma tawagar likitoci sun shaida masa cewa, yanayin lafiyar Mandela ya tsananta cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

Zuma ya ce, likitocin suna duk kan abin da ya kamata wajen ganin yanayin nasa ya inganta, kana suna bayar da tabbacin cewa, ana kula da shi yadda ya kamata, inda ya yi kira ga 'yan kasar ta Afirka ta Kudu da duniya baki daya wajen yiwa Mandela addu'ar samun sauki.

Idan ba a manta ba, a ranar 8 ga watan Yuni ne aka kwantar da Mandela a asibitin birnin Pretoria sakamakon cutar huhu, sannan a ranar 27 ga watan Maris, an kwantar da shi, bayan da likitoci suka gano cewa, yana fama da cutar nimoniya, bugu da kari, an kwantar da Mandelan a watan Disamban bara sakamakon cutar ta huhu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China