in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan da MDD na nazari kan matsalar yankunan Darfur da Kordofan
2013-07-05 10:07:44 cri

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya tattauna a ranar Alhamis tare da jami'in MDD dake kula da ayyukan tabbatar da zaman lafiya, mista Herbe Ladsous kan matsalar da ake fuskanta a yankunan Darfur da Kordofan, a wani labari da kamfanin dillancin labarai na SUNA ya rawaito. Taron ya mai da hankali kan batun sake sabunta wa'adin tawagar tarayyar kasashen Afrika da MDD a yankin darfur (MINUAD), in ji mista Ladsous. Haka ma ya ce, taron ya kuma duba cigaban da aka samu a yankin Darfur, tare da fatan ganin an gaggauta aiwatar da kundin Doha kan zaman lafiya a Darfur (DDPD). Ya kuma bayyana cewa, taron ya tattauna kan dangantaka tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu da kuma matsalar jin kai a jihohin Kordofan ta Kudu da Blue Nile.

Jami'in na MDD ya jaddada goyon bayansa ga duk kokarin da zai taimaka wajen samar da zaman lafiya ta hanyar yin shawarwari cikin sulhu da siyasa.

Tawagar MINUAD ta karbi aikin shimfida zaman lafiya a Darfur a ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2007 tare da niyyar jibge sojoji da 'yan sanda dubu ishirin da shida domin kare fararen hula a wannan yanki da suka sha wahalhalun yakin basasa tun shekarar 2003. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China