A jiya Talata 4 ga wata, babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon da shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU madam Nkosazana Dlamini-Zuma suka sanar da nada Laftanar Janar Paul Ignace Mella, 'dan kasar Tanzaniya a matsayin sabon kwamandan rundunar tsaro ta kiyaye zaman lafiya ta MDD da AU a Darfur.
Laftanar Mella zai maye gurbin Laftanar Janar Patrick Nyamvumba na kasar Rwanda, wanda ya kammala wa'adin aikin a ranar 31 ga watan Maris na wannan shekarar, in ji wata sanarwa da aka fitar daga ofishin kakakin majalissar.
Sanarwar ta yi bayanin cewa, babban magatakardan ya nuna matukar godiyar majalissar ga Laftanar Nyamvumba bisa ga sadaukar da lokacinsa da ya yi wajen aiki tukuru a cikin wa'adin aikinsa, sannan sanarwar ta kara da cewa, sabon kwamandan Laftanar Mella zai fara aiki tare da gabatar da kwarewarsa na tsawon lokaci da ya yi yana aikin soja a Tanzaniya, wanda a baya bayan nan shi ne babban hafsan tsaro a bangaren leken asiri a Dares Salam.
Kamin wannan aikin, har ila yau Janar Mella ya rike manyan mukamai da suka hada da darektan sirri na kasashen waje, a sojan kasar ta Tanzaniya, babban kwamanda na bataliyan ofishin MDD dake Liberiya, sannan kuma ya taba zama babban mai ba da shawara ta fuskar tsaro a ofishin jakadancin Tanzaniya dake Uganda.
Janar Mella wanda aka haife shi a garin Moshi a shekarar ta 1955 ya yi digiri na biyu a sashen tsaro da dabaru, a makarantar tsaro ta kasar Afrika ta Kudu.
Shi dai rundunar tsaro ta kiyaye zaman lafiya ta MDD da aka kafa ta ranar 31 ga watan Juli na shekarar ta 2007 ita ce rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalissar mafi girma a duniya, kuma babban aikin shi shi ne kare lafiyar fararen hula, duk da cewa yana kula da taimakon ba da agajin jin kai, karfafa bin doka da oda tare da tabbatar da kare hakkin dan adam. (Fatimah)