Wani wakilin gwamnatin kasar Sin ya gana ranar Lahadi da jami'an gwamnatin kasar Sudan a birnin Khartoum dangane da dangantakar kasashen biyu da kuma yanayin da ake ciki a Darfur, in ji ofishin jakadancin kasar Sin ranar Litinin.
A fadin sanarwa da ta fito daga ofishin jakadancin kasar Sin a Khartoum, wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin a kan batutuwan Afirka Zhong Jianhua ya gana da mataimakin shugaban kasar Sudan Al-Haj Adam Yosif da karamin ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Rahamtalla Mohammed Usman ranar Lahadi.
Bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi a kan dangantakarsu, yadda abubuwa suke tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu da kuma halin da ake ciki a yankin Darfur.
A kuma ranar Lahadin har wa yau, Zhong ya gana da wakilin hadin gwiwa na musamman na aikin kawo zaman lafiya na kungiyar hada kan kasashen Afirka da MDD a Darfur, Mohammed Ibn Chambas dangane da yanayi a cikin yankin.(Lami)