in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rubzawar wata mahakar zinari a yankin arewacin Darfur ta hallaka mutane sama da 60
2013-05-03 09:51:13 cri

Wasu rahotanni daga jihar arewacin Darfur ta kasar Sudan sun bayyana cewa, wasu ma'aikatan masana'antar hakar zinari dake Al-Siraif sama da 60 sun rasa rayukansu, bayan da ramin da suke aiki ciki, dake yankin Jabel Amer ya rubza.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Janar Al-Sir Ahmed Omer ne, ya tabbatar da faruwar wannan lamari ga kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua.

Tun da fari dai wata kafar watsa labarun kasar ta bayyana cewa, wasu mahakan zinari 60 sun makale a wannan mahaka, a ranar Litinin 29 ga watan Afrilun da ya gabata, bayan da kofar ramin da suke ciki ta toshe sakamakon rubzawar kasa.

Tuni dai kwamishina mai lura da yankin Haroun Al-Hussein ya gargadi mutane, don gane da hadarin dake tattare da wannan aiki na hakar zinari a yankin na Jabel Amer. Cikin watan Fabrairun da ya gabata ma dai mutane 53 sun rasa rayukansu, baya ga wasu 83 da suka jikkata a wannan yanki, sakamakon fadan kabilanci tsakanin manyan kabilun wurin biyu, lamarin da ya sanya mahukuntan kasar shiga tsakani, tare da ba da umarnin dakatar da hakar zinari a yanki na Jabel Amer.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China