in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Sudan sun kashe 'yan tawayen Darfur guda 3
2013-04-24 10:47:52 cri

Gidan rediyon Sudan ya ambato sojojin Sudan na bayyanawa a ranar Talata cewa, sun kashe 'yan tawayen SLA bangaren Minni Minnawi da ke kudanin yankin Darfur, bayan wani kazamin fada tsakanin bangarorin biyu.

Gidan rediyon ya ruwaito kakakin sojojin Sudan Al-Sawarmy Khalid Saad na cewa, 'Sojojin na Sudan sun rutsa da ragowar bangaren 'yan tawayen na Minna Minnawi ne a yankin Hijair Tonno, kana suka kashe uku daga cikin kwamandojinsu."

Bugu da kari, sojojin sun kuma lalata motocin 'yan tawayen guda 15 tare da kwace makamai da alburusai masu tarin yawa daga hannunsu. Kakakin sojojin ya ce, an kashe wasu daga cikin sojojin yayin da wasu kuma suka jikkata, yana mai nanata cewa, sojojin za su ci gaba da gudanar da daukar matakai, har sai an samu zaman lafiya a yankin na Darfur.

Kungiyoyin 'yan tawaye ciki har da JEM da SLA bangaren Minna Minnawi da Abdul Wahid Nur, sun yi watsi da sasantawa da gwamnatin Sudan na wanzar da zaman lafiya a shiyyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China