Babbar jami'ar ofishin kula da 'yan gudun hijira na MDD Valerie Amos ta nuna matukar damuwarta game da yadda yankin Darfur na kasar Sudan har yanzu ba ta iya dogaro da kanta, tana mai nuna bukatar dake akwai na hadin gwiwwa mai karfi tsakanin masu ayyukan jin kai da na ci gaba.
Madam Amos wadda a yanzu haka take ziyarar aiki na yini 4 a Darfur ta lura da cewa, shekaru 10 da aka yi ana ba da kayayyakin jin kai a yankin, akwai matukar damuwa ganin yadda har yanzu kungiyoyin ba da agaji na yankin suka kasa tabuka komai na taimakon al'ummarsu ga samun abin dogaro da kai, kamar yadda mataimakin kakakin MDD Eduardo del Buey ya sanar ma manema labarai a ganawarsu na duk rana.
Bayan da ta gana da wadanda suka rasa matsuguni a sansanin Zam Zam dake arewacin Darfur, babbar jami'a Valerie Amos ta bukaci kyakkyawan hadin gwiwwa tsakanin kungiyoyin ba da agaji da na ayyuka ganin yawan mutanen da wannan rikici ya shafa wanda aka yi shekaru 10 ana yinsa ke ci gaba da karuwa sannu a hankali, yanzu haka a cikin watanni 6, an yi ma mutane 10,000 rajista a sansanin Kalma can waje da garin Nyala, babban birnin kudancin Darfur wanda daman yake da yawan 'yan gudun hijira kusan 82,000 da yawancinsu suka dade suna zama a garin.
'Yan tawayen Darfur da suka rabu zuwa kungiyoyi daban daban tun lokacin da suka fara tawaye a shekara ta 2003, suna kawo cikas ga duk wani ayyukan cigaba da za'a gabatar a wannan wuri tare da kawo barazanar tsaro a yammacin Sudan, inda MDD ta yi kiyasin cewa, mutane kusan 300,000 sun rasa rayukansu tun lokacin da aka fara wannan kazamin fadan. Akwai rahotannin ci gaba da fada mai tsanani tsakanin 'yan tawayen da gwamnatin kasar Sudan tun farkon wannan shekarar a wannan yankin.(Fatimah)