in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon MDD a Darfur ya kammala rangadin duba wasu jihohin da ke shiyyar
2013-05-02 10:18:35 cri

Kakakin magatakardar MDD Martin Nesirky ya fada a ranar Laraba 1 ga watan Mayu cewa, shugaban tawagar kungiyar AU da MDD a yankin Darfur na kasar Sudan(UNAMID), wakilin hadin gwiwa na musamman Mohammed Ibn Chambas, ya kammala jerin rangadin jihohi biyar da ke yankin, don nazarin yanayin tsaro, harkokin jin kai da kuma siyasa.

Martin Nesirky ya fada yayin taron manema labarai cewa, ziyarar manzon na MDD ta kwanaki 8 daga ranar 22 zuwa 30 ga watan Afrilu, har da ganawa da wakilan al'ummomin da rikici ya wargaza, sarakunan gargajiya, hukumomin jihohin da kuma ma'aikatan UNAMID.

Ziyarar Chambas zuwa yankin na Darfur, ita ce ta farko a hukumance a yankin a matsayinsa na shugaban UNAMID, mukamin da ya kama aiki a ranar 1 ga watan Afrilun shekara ta 2013.

A farkon wannan makon, mataimakin shugaban MDD mai kula da sashen ayyukan wanzar da zaman lafiya Herve Ladsous, ya ce, babban abin damuwa shi ne yadda fada ya kasance a yankin na Darfur sakamakon fito na fito da sojoji da kuma al'ummomi ke yi, lamarin da ya yi sanadiyar sama da mutane dubu 200 suka rasa gidajensu, ciki har da mutane dubu 24 da suka yi kaura zuwa kasar Chadi, adadin da ya haura na shekarar da ta gabata.

Bayan wannan sanarwa, Mr. Chambas ya fada yayin rangadin nasa cewa, hanya daya ta magance rikicin yankin Darfur, ita ce samar da zaman lafiya, ta yadda jama'a za su zauna ba tare da wata fargaba ko tursasawa ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China