in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron karawa juna sani kan muhimmancin tsaro a Najeriya
2013-06-25 15:21:58 cri

Ranar Litinin 24 ga wata ne aka yi wani taron karama juna sani na yini guda, dangane da muhimmancin kiyaye tsaro a halin yanzu a Najeriya a otel din Transcorp dake Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

An yi wannan taro ne a ranar Litinin 24 ga watan nan, da nufin tattaunawa kan muhimmancin tsaro, da wayar da kan jama'a kan hanyoyin kaucewa duk wani hadarin da ka iya faruwa a halin yanzu a kasar. Magatakarda ta dindindin a ofishin sakatariyar gwamnatin tarayyar Engr. Esther G. Gonda, ta bayyanawa mahalarta wannan taro dalilin shirya shi: "mun kawo shugabanni na jama'a ta wajen addini, ka ga sarakuna sun zo nan wurin yau, da manyan ma'aikatan kamfanoni iri-iri,sun zo nan wurin. Abin da ya sa mun kawo su, muna so mu tattauna domin a kan wane irin matakai za mu dauka, in dai irin wadannan ababai sun fada mana. Muna rokon Allah muna addu'a cewa irin wadanannan abubuwa ba za su auku ba, amma dole mu zama a shirye, in mun zama a shirye zamu iya sha maganin wannan gurin.Abinda ya kawo mu ke nan."

Engr. Esther G. Gonda ta kuma bayyana muhimmancin wannan taro, inda ta ce: "muna wannan taro kowa ya san halin da muke ciki a najeriya, kuma ba a najeriya kadai ba, zan ce duk duniya, muna fama da irin tashin hankali a ko ina, ya kamata mu tattauna, mu ga abin da za mu yi a kai.".

Wani mahalarcin taron, Engr. Daniel Balarabe Ganbo, ma'aikaci a hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, shi ma ya tofa albarkacin bakinsa dangane da wannan taro, musamman ma kan matakan da jama'a za su iya dauka, don kauce ma hadarin da ka iya tasowa a zaman rayuwarsu, inda ya ce:"E, wannan taro yana da kyau domin taro ne na fadakarwa akan yadda zamu iya mu tabbatar da cewa idan akwai hadari, mutane ba su jikkata ba, a dalilin matakai da ya kamata a dauka, domin a tabbatar da cewa wannan abin da ka iya kawo hadari, an kawar da shi, ko kuma ainihin al'ummar wadda za ta zama ta samu lahani, ita kanta ta kau, daga wannan wuri. Fadakarwa shi ne ake kokari a fadakar da al'umma su tabbatar da cewa na daya, inda suke, muhallansu suna da kyakyawan tsaro, su da kansu suna da kyakyawan tsaro domin lafiyar kansu, cewa a duk inda suke sun tabbatar da suna sane da muhallinsu koko yanayin da suke ciki.Idan akwai hadari, su kauce daga wannan wuri, idan ko babu hadari, ka ga suna iya bajewa, su baje kolinsu, su sheke ayansu, su ji dadin zama a wurin."

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China