in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Morsi na Masar ya ce, ba gudu ba ja da baya
2013-07-03 09:54:20 cri

Yayin da 'yan adawa da masu ra'ayin kawo sauyi ke ci gaba da zanga-zangar nuna rashin amincewa da salon jagorancinsa, a hannu guda kuma magoya baya ke ci gaba da ba shi kariya, shugaba Mohammed Morsi na Masar ya ce, ko alama ba shi da niyyar sauka daga karagar mulkin kasar.

Cikin wani jawabinsa na baya-bayan nan da gidajen talabijin na kasar suka yada, Morsi ya ce, ba abu ne mai yiwuwa a jingine halascin da kundin mulkin kasar ya baiwa gwamnatin kasar mai ci ba. Shugaban kasar ta Masar ya kuma yi kira ga rundunar sojin kasar da ta janye batun wa'adin da ta gindaya na warware takaddamar siyasa dake aukuwa yanzu haka a kasar, tare da kira ga al'ummar kasar fararen hula, da kada su dauki matakin farma sojoji ko 'yan sanda.

Shugaba Morsi ya zargi birbishin magoya bayan tsohuwar gwamnatin kasar da ta gabata, da kokarin hana ruwa gudu, a kokarin da ake yi na wanzar da mulkin dimokaradiyya. Daga nan sai ya bayyana damuwarsa ga halin da al'ummar kasar ke ciki, yana mai cewa, zai tsaya tsayin daka, wajen ganin ya hana zub da jinin wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai, ministan tsaron kasar ta Masar ya baiwa dukkanin masu ruwa da tsaki a rikicin siyasar kasar wa'adin kwanaki biyu don warware takaddamar dake tsakani, kafin daukar matakin soji, a cewarsa, shi ne mataki na karshe da za a iya dauka na kaucewa tsundumar kasar cikin yakin basasa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China