in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu ra'ayin kishin Islama a Masar sun bayyana adawa da daukar matakin soji
2013-07-02 10:11:24 cri

Gungun hadakar jam'iyyun 'yan kishin Islama a Masar, ciki hadda kungiyar 'yan uwa Musulmi, sun nuna rashin amicewarsu da batun shigar rundunar sojin kasar rikicin siyasar da a yanzu haka ke ciwa mahukunta tuwo a kwarya.

Jam'iyyun 'yan kishin Islaman sun bayyana goyon bayansu ga daukar dukkanin matakan shawo kan matsalar siyasa dake addabar kasar bisa tanajin doka, yayin da a hannu guda suka bayyana adawa ga abin da suka kira yunkurin haramta halastacciyar gwamnatin kasar mai ci ta hanyar daukar matakan da za su kai ga juyin mulki.

Wata sanarwa da aka yada ta gidan talabijin na kasar ta Masar, ta bayyana adawar tsagin masu goyon bayan gwamnatin mai ci da daukar matakin soji, tare da kira ga al'ummar kasar da su yi dafifi kan titunan kasar, domin kare halascin gwamnatin mai ci. Wannan sanarwa dai na zuwa ne kwana guda bayan jawabin ministan tsaron kasar Abdel-Fattah Al-Sisi, wanda ya baiwa jam'iyyun siyasar kasar kwanaki biyu, domin warware matsalolin da ake fuskanta, idan kuwa hakan ya gagara, a cewarsa, sojoji za su bullo da wani tsarin mai da kasar kan turba, domin kyautata makomar al'ummar kasar.

Sisi ya ce, wannan ne mataki na karshe da za a iya dauka wajen biyan bukatun al'ummar kasar, tare kuma da magance matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa. Za kuma a yi hakan ne da tallafin dukkanin masu ruwa da tsaki, da jam'iyyun siyasa ba tare da nuna wariya ba.

Sai dai a wani batu mai alaka da wannan, kakakin rundunar sojin kasar Ahmed Ali, ya bayyana rashin dacewar gudanar da juyin mulkin soji, yana mai cewa, hakan ya sabawa managarcin tsarin aikinsu. Ali ya kara da cewa, kalaman ministan tsaron kasar na nuni ga yunkurin shiga harkokin da suka shafi fararen hula.

A yanzu haka dai, masu adawa da gwamnatin shugaba Morsi na nuna goyon bayansu ga kalaman ministan tsaron kasar, yayin da kuma daukacin magoya bayan Morsi ke taruruwa sassan biranen kasar, domin nuna masa goyon baya, tare da yin Allah wadai da wancan batu na ministan tsaron kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China