Babbar majalisar dattijai wato Choura ta kasar Masar ta amince a ranar Lahadi da tsarin dokar zabe dake kulawa da zabubukan 'yan majalisa, a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA ya rawaito.
Kwamitin Choura ya amince ga kara yawan mambobin majalisar wakilan kasar zuwa mambobi 588, da kuma na kujerun gwamnonin da ba su da yawan wakilci zuwa shida kowane. Ministan Masar kan harkokin shari'a da na 'yan majalisa, Hatem Begato, ya tabbatar da cewa, wadannan sauye-sauye na da manufar tabbatar da ganin ko wadannen kujerun gwamnoni ba za su wuce shida ba, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Kudurorin da aka canja son kasance kawai bisa nuna wakilci cikin adalci a cikin yankunan zabe, da kawar da hana amfanin kalmomin addini wajen yakin zabe da 'yancin shugaban kasa na tsawaita ko rage lokacin zabe. (Maman Ada)