Kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA, ya ruwaito ministan tsaron kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi na cewa, hakkin sojoji ne su shiga tsakani don hana kasar shiga munanan rikice-rikice, fadawa rikicin cikin gida da na kabilanci.
Ministan tsaron, ya yi kira ga dukkan bangarorin siyasar kasar, da su daidaita a tsakaninsu don kare martabar kasarsu, ganin cewa, yanzu saura mako guda, a yi gangamin da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga watan Yuni, don kira ga shugaba Mohammed Morsi da sauka tare da shirya zaben shugaban kasa kafin ranar da aka shirya.
Ya ce, bambancin da ake fuskanta a tsakanin al'ummar kasar game da kundin tsarin mulkin kasar, babbar illa ce ga kasar Masar, kuma wajibi ne al'ummar kasar su daidaita ta, yana mai cewa, wannan bambanci zai kawo illa ga tsaron kasa.
Don haka ya nanata cewa, hakkin sojojin kasar ne su kare rayukan jama'a. (Ibrahim)