Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi, ya yi kira da kafa hukuma mai zaman kanta, da za ta gudanar da kwaskwarima ga kundin mulkin kasar da hadin gwiwar dukkanin jam'iyyun siyasa da sassan masu ruwa da tsaki.
Wannan dai tsokaci na shugaba Morsi na zuwa ne 'yan kwanaki kadan kafin zuwan ranar 30 ga wata, ranar da zai cika shekara guda cur a kan karagar mulki, ranar da kuma 'yan adawa a kasar suka sha alwashin yin gagarumar zanga-zangar nuna kin jinin salon mulkinsa. Jawabin nasa da gidan talabijin mallakar kasar ya yada ranar Laraba 26 ga wata, ya kuma kunshi umarnin daukar matakan dakile yunkurin wadanda shugaban ya kira masu san tada hankulan al'ummar kasar.
Har ila yau, Morsi ya bayyana bukatar shigar matasa cikin harkokin jam'iyyun siyasar kasar. Bisa burin gwamnatin na sanyaya zukatan masu kudurin gudanar da zanga-zanga a kasar, shugaban kasar ya kuma umarci daukacin gwamnoni da ministocinsa, da su nada mataimaka matasa da shekarunsu ba su wuce 40 da haihuwa ba. Kana ya ba da umarnin kafa wata hukuma ta musamman, da za ta dauki nauyin sasanta bangarorin da ba-sa-ga-maciji da juna a kasar. (Saminu)