in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan kungiyar adawa a Masar na yiwa Morsi matsin lamba domin gabatar da zabe da wuri
2013-06-28 10:45:00 cri

A ranar Alhamis da yamma, babbar kungiyar adawa ta kasar Masar, National Salvation Front (NSF), ta bukaci shugaba Mohammed Morsi da ya gudanar da zaben shugaban kasa da wuri.

Kungiyar ta yi kira ga shugaba Morsi da ya saurari ra'ayin masu adawa, ya kuma mai da martini kan bukatunsu na gabatar da zaben shugaban kasar da wuri, domin a samu cimma manufofin juyin juya hali na shekarar 2011 a kasar, wanda ke da nufin tabbatar da adalci.

Sanarwar ta bayyana cewa, miliyoyin 'yan kasar Masar za su yi tururuwa zuwa wuraren gabatar da zanga-zangar lumana da za'a yi ranar 30 ga watan Yuni, domin nuna burinsu na maido da juyin juya halin, kan turbar da aka kudurta.

Masu fafutuka da kungiyoyin adawa suna ta shirin gabatar da gagarumin zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Morsi ran 30 ga watan nan, rana da zai cika shekara daya kan kujerar mulki, inda za su bukace shi ya sauka.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, za'a nada gwamnatin wucin gadi wacce za ta sake tsara kundin dokokin kasar, bullo da dokoki, gami da shirya sulhu tsakanin sassan kasar baki daya.

Kafin lokacin zanga-zanga na ranar 30 ga watan Yuni, shugaba Morsi shi ma ya yi tayin kafa wani kwamitin da zai yi wa kundin dokokin kasar gyara, kunshe da daukacin kusoshin siyasa da jam'iyyu, da kuma nada wani kwamitin da zai yi shirin sulhu na kasa.

To amma mafi yawan jama'a sun dau wannan magana tasa da cewa, ba da gaske yake yi ba, kuma tamkar ba'a ne ma ga matsalolin baki daya. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China