Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi, ya bayyana hawa teburin shawarwari a matsayin hanya daya tilo da za a bi, wajen warware matsalolin siyasar dake addabar kasar.
Shugaban ya yi wannan tsokaci ne dai dai lokaci da ake tsaka da babbar zanga-zangar nuna kin jinin salon mulkinsa a birnin Alkahira, da ma wasu lardunan kasar, inda kuma a hannu guda suna magoya bayan gwamnatin mai ci ke gudanar da tasu zanga-zangar nuna goyon baya.
Shugaba Morsi ta bakin kakakinsa Ehab Fahmi, ya bayyana amincewarsa da yancin bayyana ra'ayin 'yan kasa bisa tsarin da doka ta tanada, yana mai kore rade-raden yiwuwar amfani da jami'an soji domin murkushe masu zanga-zangar. A cewarsa, aikin dakarun sojin kasar ya takaita ne kawai ga kare al'ummar kasa da kuma iyakokinta, ko da yake dai a makon da ya gabata, an jiyo ministan tsaron kasar, na bayyana wajibcin sanya hannun rundunar sojin kasar, domin kaucewa dilmiyar kasar cikin mawuyacin hali na yakin basasa.
A wani ci gaban kuma kakakin fadar shugaban kasar ta Masar Ehab Fahmi, ya karyata rade-raden da ake yi cewa, wai za a rushe gwamnatin da firaministan kasar mai ci Hesham Qandil ke jagoranta, yana mai cewa, wannan batu ne da ba shi da tushe balle makama. (Saminu)