Kotu a kasar Masar a jiya Alhamis ta yanke shawarar goyon bayan dokar ta baya da ta umurci da a saki tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak bisa binciken da aka yi masa na azurta kansa ta haramtaciyar hanya, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar MENA.
Kotun saurarkon manyan laifuka ta kasar ta ki sauraron rokon da kotun manyan laifuka dake arewacin Masar ta gabatar na kada a saki tsohon shugaban na wani 'dan lokaci bisa zargin da ake masa na azurta kansa ta haramtacciyar hanya.
A makamancin haka, a tsakiyar watan Afrilu, wata kotu ta yanke shawarar sakin Mubarak din na wani 'dan lokaci saboda zarginsa da hannu a kissan da aka yi ma masu zanga-zanga a watan Janairun shekara ta 2011 wanda ya yi sanadiyar hambarar da gwamnatinsa, sai dai kuma tsohon shugaban kasar zai ci gaba da zama a tsare bisa zargin musamman yin sama da fadi da dukiyar kasa da aka fitar domin gyaran fadar shugaban.
Mubarak wanda aka yanke masa hukunci rai da rai a watan Yuni na shekarar 2012, amma ya daukaka kara, kotun ta saurarin kara sa ta kuma yanke shawarar sake mashi wani shari'ar da aka fara a watan mayun bana.yanzu za'a sake sauraraon karar tasa a ranar 6 ga watan yuli mai zuwa. (Fatimah)