Rahotanni daga fadar gwamnatin kasar Afirka ta Kudu na bayyana cewa, tsohon shugaban kasar, kuma 'dan gwagwarmayar yaki da nuna wariyar launin fata Nelson Mandela, na ci gaba da samun sauki a asibiti, inda yake kwance kimanin mako guda.
Shugaban kasar mai ci Jacob Zuma ne ya bayyana hakan a Newcastle dake lardin Kwazulu-Natal, yayin da ake tsaka da bikin ranar matasa. Shugaba Zuma ya kuma yi kira ga daukacin 'yan kasar tasa, da su sanya Mandela a cikin addu'o'insu, tare da fatan samun cikakkiyar warakarsa. Mandela da zai cika shekaru 95 da haihuwa a wata mai zuwa na ci gaba da samun kulawar likitoci tun daga ranar 8 ga wannan watan da muke ciki, sakamakon sake dawowar ciwon huhu da ya dade yana fama da shi. Tsohon shugaban dai na ci gaba da fama da wannan larura tun daga watan Disambar da ya gabata, lamarin da a ko da yaushe ke jan hankalin al'ummar kasar ta Afirka ta Kudu. (Saminu)