in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da Sudan ta Kudu sun nanata aniyarsu dangane da ci gaba da tattaunawa
2013-07-02 09:47:58 cri

A ranar Litinin, kasashen Sudan da Sudan ta Kudu suka nanata aniyarsu na yin tattaunawa da kulla yarjejeniya don warware batutuwa dangane da banbance-banbance tsakaninsu da kuma shan alwashin kauracema ba da tallafi ko kuma ba da mafaka ga 'yan bindiga.

Kasashen biyu sun kammala tattaunawar ne a birnin Khartoum. Bayan ganawar ta hadin gwiwa, kasashen biyu sun ba da jawabin bayan taro inda a ciki suka nanata kudurinsu na amincewa da shawarwari da hukumar sa ido ta kungiyar AU kan Sudan (AUHIP) ta gabatar dangane da matsala ta baya bayan nan tsakanin kasashen biyu.

Sun yi alkawarin yin tattaunawa ta hadin gwiwa ba tare da wani ra'ayi sabanin wanda AUHIP ta gabatar ba.

A halin da ake ciki kuma, kasashen biyu sun bayyana aniyarsu na kammala yarjejeniya kan batutuwan zaman lafiya, a fannoni kamar kan iyakoki da kuma kan batun yankin Abyei da suke takaddama a kai.

An sake samun tashin hankali tsakanin kasashen biyu ne bayan da kasar Sudan ta dakatar da fitar da man kasar Sudan ta Kudu ta cikin bututunta, inda ta zargi Juba da mara bayan 'yan tawayen 'Revolutionary Front Alliance', wacce ke yakar gwamnatin Khartoum. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China