Kwanan baya, kasar Sudan ta hana kasar Sudan ta Kudu ta yi amfani da bututun man fetur da ke kasar domin sayar da man fetur zuwa ketare. Dangane da lamarin, Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a ran 13 ga wata a nan Beijing cewa, tabbatar da samar da man fetur da kuma sayar da shi zuwa ketare yadda ya kamata daga Sudan ta Kudu ta shafi babbar moriyar kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki, haka kuma zai yi tasiri kan huldar da ke tsakaninsu duka.
A don haka kasar Sin take kira ga kasashen 2 da su kasance cikin nitsuwa da yin hakuri, su nuna wa juna kulawa kan muhimman batutuwan da suka mai da hankali a kai. Ya kamata su aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma a baya, a kokarin kau da sabanin da ke tsakaninsu yadda ya kamata da kuma kiyaye huldar da ke tsakaninsu ta hanyar yin tattaunawa da shawarwari na cude-ni-in-cude-ka.(Tasallah)