in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya bayyana dabarar da za ta taimakawa kasashen Afrika samun wutar lantarki
2013-07-01 11:06:08 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya sanar a ranar Lahadi da dabarar da ta shafi dalar Amurka biliyan bakwai dake da manufar rubanya hanyar samar da wutar lantarki a nahiyar Afrika.

A yayin da yake jawabi a jami'ar Cape Town, Obama ya bayyana cewa, wannan dabara za ta rataya wajen fadada samar da wutar lantarki a cikin kasashen Afrika shida da suka hada da Habasha, Ghana, Kenya, Liberia, Najeriya da Tanzania, kuma karin taimakon dalar Amurka biliyan tara za su fito daga wasu kamfanonin Amurka masu zaman kansu kamar kamfanin General Elecrtic da na Symbion Power.

Wadannan taimako sun yi kasa sosai bisa ga dalar Amurka biliyan 300 da cibiyar makamashi ta duniya (AEI) take bukata domin cika aikinta na samar da wutar lantarki ga kowa a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara nan da shekarar 2030.

Shugaba Obama ya dauki alkawari da cigaba da zuba jarin Amurka a cikin tsare-tsaren kiwon lafiya, musammun ma kan tsarin yaki da ciwon Sida. Haka kuma ya gayyaci kasashen Afrika wajen yin aiki tare domin kawo karshen yake-yake da tashe-tashen hankali a nahiyar. A karshe Obama ya kai ziyara a tsibirin Robben inda tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela ya yi zaman yari na tsawon shekaru goma sha takwas. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China