in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria za ta gina cibiyar samar da lantarki ta nukiliya nan da shekarar 2025
2013-05-20 10:00:13 cri

Hukumomin kasar Algeria su bayyana aniyarsu ta gina cibiyar samar da lantarki daga makamashin nukiliya nan da shekarar 2025, aikin da ake fatan zai kawo karshen matsalar karancin wutar lantarkin dake addabar kasar, ya kuma ba da damar fadada shirin gwamnatin kasar na inganta samar da lantarkin.

A cewar ministan ma'aikatar makamashi da ma'adanai na kasar Yousef Yousfi, wannan aiki zai zamo irinsa na farko a kasar, kuma ma'adanin Uranium da kasar ta Algeria ke da shi, wanda yawansa ya kai tan 29,000, ya isa a kafa tashoshin lantarkin har guda 2 a lokaci guda, wadda ko wacce ka iya samar da karfin lantarki har mega-watt 1000 a tsahon shekaru 60.

Kamfanin dillancin labarai na APS ya rawaito ministan na cewa, sabuwar cibiyar fasahar nukiliyar da aka kafa a baya-bayan nan, za ta dauki nauyin horas da ma'aikatan da za su lura da ayyukan tashar nukiliyar, da zarar an kammala ginin ta.

Tun dai a watan Nuwambar shekarar 2008 ne kasar ta Algeria, ta bayyana cewa, ta fara shirin gina wannan cibiya ta makamashin nukiliya kashin farko, wanda za a kammala a shekarar 2020, kuma za a rika kafa irin wannan tasha guda daya a bayan shekaru biyar-biyar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China