Akwai manoma da yawansu ya kai miliyan 900 a kasar Sin, wadda ke da yawan al'umma biliyan 1.3 a kasar. Bayan da zaman rayuwar kauyuka ya samu kyautatuwa, manoma da dama sun koma gidajensu, kana an kara aiwatar da manufar samar da kayayyakin lantarki da aka yi amfani da su a gida, da injuna, da motoci a kauyuka, an kuma kara bukatun wutar lantarki a kauyuka. Amma, duk da haka, an samu koma baya wajen kafa tirakun lantarki a kauyuka, haka kuma, akwai wasu wurare da har yanzu babu wuta a cikinsu, sabo da akasarin tirakun lantarki a kauyuka sun lallace, inda aka samu hasarar wutar lantarki, lokaci ya yi da za a inganta su, don kyautata aikin samar da wutar lantarki, da biyan bukatun jama'a wajen amfani da wutar lantarki a kauyukan kasar.
Yanzu, kasar Sin na kokarin gina sabbin kauyuka. Manazarta sun bayyana cewa, nan gaba, gwamnatin Sin za ta kara kebe kudade don gina manyan ababen more rayuwa a kauyuka.(Bako)