in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu zuba jari na rige-rigen sayen sabbin cibiyoyin samar da wutar lantarki a Najeriya
2013-06-05 10:01:07 cri

Masu zuba jari sama da 40 daga ciki da wajen kasar Najeriya dake yammacin Afirka na rige-rigen mallakar cibiyoyin samar da wutar lantarki guda 10 da gwamnatin kasar za ta sayar a kokarinta na bunkasa samar da wutar lantarki wanda ke ciwa kasar tuwo a kwarya, musamman ma a fuskar bunkasar tattalin arziki.

A yayin wani shiri da aka kaddamar ranar Talata a Lagos, cibiyar harkokin cinikayya a kasar, na yin tallen cibiyoyin ta hanyar yawo a tituna, gwamnati ta bayyana cewa, na'urorin guda 10 baki daya za su samar da wutar lantarki mai yawan megawatts 5000.

Ana sa rai cewa, kudade da za'a samu daga sayar da cibiyoyin za'a yi amfani da su wajen sake samar da wasu na'urorin wutar lantarkin a kasar ta yammacin Afirka.

An ci karfin aikin kammala aikin gina shida daga cikin cibiyoyin yayin da ake sa ran kammala sauran nan da shekarar 2014.

Ministan makamashi na kasar Chinedu Nebo, a bayaninsa yayin shirin na kwanaki biyu da ya samu zuwan shugabannin masana'antu, jami'an gwamnati, sarakuna, masu fasaha, masu ba da shawarwari kan harkar kudade da wadanda ake sa rai za su zuba jari, ya jadadda cewa, gwamnati za ta sayar da hannun jarinta na kashi 80 cikin dari a cibiyoyin, kana harkar sayar da cibiyoyin zai kunshi cibiyar sayar da kadarori mallakar gwamnati.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China