in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cabke tsohon shugaban Chadi Hissene Habre a Dakar na Senegal
2013-07-01 10:44:17 cri

Jami'an tsaron kasar Senegal sun cabke tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habre a ranar Lahadi da safe a gidansa dake wata unguwar birnin Dakar, a cewar daya daga cikin matansa da kuma daya daga cikin lauyoyinsa bisa wani rediyo mai zaman kanta na kasar Senegal wato RFM.

An yi awon gaba da Hissene Habre tare da kai shi wani wuri. Wannan wata muzgunawa ce, in ji mai ba shi shawara Me El Hadj Diouf.

Sai dai har yanzu hukumomin kasar Senegal ba su ba da wani karin haske ba ko wani dalilin kama Hissene Habre dake gudun hijira a birnin Dakar tun lokacin da aka masa juyin mulki a shekarar 1990, bayan shekaru takwas yana mulki. Ana zargin tsohon shugaban kasar Chadi da aikata manyan laifuffukan keta hakkin bil adama, laifuffukan yaki da na cin zarafin 'dan adam, kuma za'a gurfanar da shi gaban kuliya a kasar Senegal bisa bukatar kungiyar tarayyar Afrika AU.

Bisa haka ne hukumomin kasar Senegal suka kafa a farkon wannan shekara wasu kotunan musammun na Afrika domin yi wa tsohon shugaban kasar Chadi shari'a. Haka kuma wadannan kotuna za su cigaba da gurfanar da duk mutanen dake da hannu kan laifuffukan da aka aikata a kasar Chadi tsakanin shekarar 1982 zuwa shekarar 1990. Wadannan kotuna za'a rarraba su zuwa kashi uku domin kula da bincike, shari'a da karbar bukatun daukaka kara kuma sun kunshi alkalan kasar Senegal da na sauran kasashen Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China