Kungiyar raya kogin Senegal (OMVS) ta bayyana a ranar Litinin a birnin Dakar da kaddamar da ayyukan gina madatsar ruwan samar da wutar lantarki ta Gouina a kasar Mali, mai karfin mega watt 140.
A cewar takardar sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu, matakin kaddamar da wannan aikin gini kafin karshen shekara an dauke shi a yayin taron kwamitin ministocin OMVS dake kunshe da Guinee, Mali, Mauritania da Senegal da ya gudana daga ranar Lahadi da Litinin a Dakar, babban birnin kasar Senegal.
Madatsar ruwan Gouina za ta cike sahun madatsun ruwa biyu na samar da wutar lantarki da kungiyar OMVS ta gina, su ne madatsar ruwan Manantali da aka gina a shekarar 1980 da kuma ta Felou da yanzu haka ake ginawa.
OMVS kungiya ce ta kasa da kasa da aka kafa a ranar 11 ga watan Maris na shekarar 1972 a Nouakchott tsakanin kasashen Mali, Mauritania da Senegal da burin kulawa da kogin Senegal da ya cimma tsawon kilomita dubu 289. Kasar Guinee inda wannan kogi ya fito, ta shiga wannan kungiya a shekarar 2005. (Maman Ada)