in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liu Yunshan ya gana da wasu jami'an kasar Senegal a Beijing
2013-05-09 14:39:24 cri

Liu Yunshan, babban jami'in jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC ya gana da wata tawagar jam'iyyar APR ta kasar Senegal dake karkashin jagorancin Mbaye Ndiaye, ministan kasa kuma mamban kwamitin koli na jam'iyyar APR a ranar Laraba 8 ga wata a Beijing, babban birnin kasar Sin.

Mista Liu, mamba na kwamitin din din din na cibiyar siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, ya bayyana cewa, dangantaka tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta shiga wani sabon yanayin bunkasuwa.

A cewarsa, huldar tsakanin kasar Sin da kasar Senegal babban jigo ne a cikin huldar da ake tsakanin nahiyar Afrika da kasar Sin, kuma ya kamata bangarorin biyu su cigaba da karfafa amincewar juna da yawaita tuntubar juna tsakanin jam'iyyun siyasa da gwamnatocin kasashen biyu.

Mista Ndiaye ya bayyana cewa, kasar Senegal na darajanta ayyukan cigaba da kasar Sin da jam'iyyar CPC suka gudanar kuma kasarsa na fatan koyi da kasar Sin da CPC.

Tawagar kasar Senegal na yin wata ziyarar aiki a nan kasar Sin tun daga ranar 6 zuwa 14 ga watan Mayu bisa goron gayyatar jam'iyyar CPC. (Maman Ada) 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China