Kasar Senegal ta samu wani gibin kudi na Sefa biliyan 400 kimanin dalar Amurka miliyan 800 a bangaren ma'adinai daga shekarar 2005 zuwa ta 2012, dalilin wata alfarma dauke nauyin wasu kudaden kwastan da haraji da aka baiwa kamfanonin ma'adinai, in ji darektan harkokin ma'adinan kasar, mista Ousmane Cisse a ranar Jumma'a a birnin Dakar.
A dunkule, gibin kudin da gwamnati ta samu ya cimma kusan Sefa biliyan 401,2 da aka kashe bisa dauke nauyin harajin kwastan, wanda daga bisani gwamnati ba ta samu komai ba, illa Sefa biliyan 40 a duk tsawon wannan lokaci, in ji mista Cisse.
Mun lura cewa, ta fuskar fasaha, muhalli, kwadagon kasa, taimako ga cigaban tattalin arzikin kasa, a dunkule, bangaren ma'adinai na bukatar gyaran fuska. Akwai kura-kurai da aka gano ta ko ina, a bangaren masana'antun ma'adinai, har ma zuwa bangaren gwamnati, a cewar mista Ousmane Cisse.
Haka kuma ya kara da cewa, kwamitin sake duba yarjejeniyoyi ya bukaci a sake duba kundin ma'adinai domin kawo daidaici kan wannan kuduri da aka sanya wa hannu a shekarar 2003 dake sa ido kan ayyuka a wannan bangare. A halin yanzu, kamfanonin kasashen waje suna hakar zanari, sinadarin phosphate da na zircon a kasar Senegal. (Maman Ada)