in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu ta musunta rahotonni kan sace ma'aikatan lalata nakiyoyi 12 a Senegal
2013-05-06 10:52:54 cri

Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta musunta a ranar Lahadi da rahotonnin wasu kafofi dake bayyana cewa, an sace wasu ma'aikatan kasar 12 dake aikin lalata nakiyoyi a kasar Senegal.

'Wannan ba gaskiya ba ce. Ba wani 'dan Afrika ta Kudu da aka sace a kasar Senegal.' in ji mista Clayson Monyela, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Afrika ta Kudu.

A cewar wadannan kafofi, wasu ma'aikatan kamfanin lalata nakiyoyi na Mechem na kasar Afrika ta Kudu goma sha biyu ne aka sace a yankin Casamance na kasar Senegal, inda gungun dakarun 'yan aware na MFDC suke dagar neman 'yancin yankinsu tun daga shekarar 1982.

An rasa duriyar ma'aikatan kamfanin Mechem tun ranar Jumma'ar da ta gabata, kuma tun daga wannan lokaci ne hukumomin wannan yanki suke aikin ganin an sako su, a cewar wasu majiyoyi masu tushe daga kasar Senegal.

Da yake hira da kamfanin dillancin labarai na kasar Senegal, mista Fred Weyers, darektan shiyya na Mechem dake cibiya a birnin Pretoria, ya bayyana cewa, wadannan ma'aikata 12 sun bace tun ranar Jumma'ar da ta gabata, kuma ana zaton suna hannun 'yan tawayen MFDC. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China