in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Masar ba za ta shiga harkokin gidan wata kasa daban ba, in ji mahukuntan kasar
2013-06-17 10:07:20 cri

Wata majiya mai tushe ta rundunar sojin kasar Masar ta yi karin haske kan matsayar kasar don gane da rikicin da ke ci gaba da addabar kasar Sham, tana mai cewa, rundunar ba za ta tsoma baki cikin al'amuran cikin gidan wata kasa ba. Kamfanin dillancin labarai na MENA ne dai ya rawaito wani babban jami'in rundunar na cewa, ayyukan sojin kasar ya takaita ne ga tsaro, da kuma kare rayukan al'ummarta.

Wannan dai furuci ya biyo bayan kalaman shugaban kasar ta Masar Mohammad Morsi a ranar Asabar din da ta gabata, dake cewa, 'yan kasarsa da sojojinta, na goyon bayan zabin da al'ummar Sham suka yiwa kansu, ya kuma bayyana rufe ofishin jakadancin kasarsa dake Sham, tare da katse duk wata huldar diplomasiyya dake tsakanin kasar tasa da Sham. Da yake fashin baki kan wannan batu, wani jigo a kungiyar 'yan adawar kasar ta Sham dake gudun hijira a kasar Masar Momen Kouifatie, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua cewa, a ganinsa, furucin na shugaba Morsi ba ya nufin Masar na da muradin tallafawa 'yan tawayen Sham da makamai ko dabarun yaki, kamar yadda Amurka ta bayyana aniyar yin hakan. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China