Yanayin lafiyar tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela yana inda yake bai canja ba a ranar Asabar da yamma, in ji kakakin fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu, Mac Maharaj.
Mista Mandela ya sake komawa gadon asibiti a ranar Asabar bayan sake kamuwa da ciwon huhu a Pretotria, yana samun yin lumfashi da kansa, in ji mista Maharaj.
'Likitocin sun bayyana cewa, Mandela yana samun yin lumfashi da kansa, ina ganin cewa, wannan shaida ce mai gamsarwa.' a cewar mista Maharaj.
Jami'in ya bayyana da farko a ranar cewa, rashin lafiyar Mandela mai shekaru 94 ya yi kamari, amma ya tsaya daidai. A 'yan kwanakin baya, mista Mandela ya sake kamuwa da ciwon huhu, abin da ya kara tsananta halin rashin lafiyarsa tun safiyar Asabar, dole aka gaggauta kai shi asibitin Pretoria. Kuma har yanzu halin da yake ciki na daukar hankali, in ji kakakin fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu.
Mista Maharaj ya kara da cewa, kafofin watsa labarai na cigaba da nasu kokari domin ganin Mandela ya samu sauki.
A lokacin baya bayan nan, an yi ta jinyar Mandela sau da dama. Zamansa a asibiti na baya shi ne na cikin watan Maris. Wannan ciwon huhu na Nelson Mandela na da halaka da ciwon tarin da ya yi fama da shi a lokacin zamansa a gidan kurkukun tsibirin Robben, dake gabar birnin Cape na kasar Afrika ta Kudu. (Maman Ada)