in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeria ta kame wani jirgin ruwan daukan kaya makare da kayayyaki masu lahani
2013-06-21 10:12:43 cri

A jiya Alhamis 20 ga wata, jami'an sojin ruwan Nigeria suka sanar da kame wani jirgin ruwan daukan kaya mallakar kasar Belgium mai suna (mv euro cargo saleno) a jihar Ikko, makare da kayayyaki masu lahani.

Komodo Chris Ezekobe, kwamanda mai kula da tashar jiragen ruwa na Apapa ya sanar ma manema labarai cewa, an tsare mutane uku da suka hada da matukin jirgin, sannan kuma ana sa ido a kan sauran mutenen da duka suka zo tare a tsibirin Tin-Can dake Apapan..

Komodo Ezekobe ya ce, jirgin ruwan daukan kayan ya shigo kasar Nigeria ne daga kasar Belgium dauke da tsaffin firjin ruwan sanyi da aka boye su a cikin manyan motoci uku.

Ya yi bayanin cewa, bayanai na sirri daga hukumar kula da daidaicin muhalli da tabbatar da bin ka'idojin da aka shimfida, ya sanar da rundunar sojin ruwan Nigerian lokacin da jirgin ya dumfaro gaba inda aka kame su, kuma yanzu haka za'a mika jirgin ga muhukuntar kula da sha'anin jiragen ruwa da ingancinsu ta kasa NIMASA domin cigaba da bincike.

Ya kara bayanin cewa, hukumar ta NIMASA da sauran hukumomin gwamnati za su binciki wannan jirgi domin tabbatar da ainihin abin da ya dauko. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China