Tarayyar Najeriya ta dauki niyyar horar da sojoji 3000 domin yaki da ta'addanci da bore, in ji rundunar sojojin kasar a ranar Alhamis.
Mista Ibrahim Attahiru, darektan hulda da jama'a na rundunar sojojin kasar, ya tabbatar da wannan shiri a yayin wani taron manema labarai na wata wata a birnin Abuja.
Jami'in sojan ya bayyana cewa, wannan horo na zuwa ne daidai da shirin kokarin mai da rundunar sojojin na Najeriya zuwa wata babbar runduna da za ta kasancewa da karfin tunkarar kalubalolin wannan zamani.
A yayin wannan horo na tsawon makwanni shida, za'a ilimantar da sojojin kan shiga cikin gine-gine, kwashe jama'a daga cikin gine-gine, yin sintiri cikin birane, yin fada ba tare da makamai ba, koyar da su kan iyar amfani da makamai da sanin 'yancin bil adama.
Haka kuma, Attahiru ya tabbatar da cewa, za a yi amfani da sabbin na'urori wajen daukar sojojin a karon farko a duk fadin kasar baki daya, kuma za a dauki sojoji 70 a ranar 22 ga watan Yunin bana. (Maman Ada)