Masanan suna ganin cewa, yayin taron shawarwari za a iya ci gaba da yin tattaunawa kan batutuwan da aka yi musayar ra'ayi yayin ganawar shugabannin kasashen biyu da aka yi a wurin gidan gonan Annenberg da ke jihar California, kamar su batun tsaron Intanet, dabarun fuskantar sauyin yanayi, tattalin arziki, cinikayya da kuma dangantakar sojojin kasashen da dai sauransu.
Shawarwarin karon nan na da muhimmiyar ma'ana ga ci gaban dangantakar kasashen biyu, sabo da zata samar da damar kara fahimtar juna tsakanin shugabannin kasashen biyu da kuma kafa dangantakar aiki mai inganci tsakaninsu. (Maryam)